A ranar Litinin din nan 7 ga wata, aka fara rajistan mutanen da za su halarci babban taron da za'a yi domin fitar da sabon kundin tsarin mulki na kasar Libya.
Babbar hukumar zabe ta kasar ce ta tsara wannan rajista a cibiyarta da kuma rassanta guda 5 a daukacin kasar. Jami'in hulda da manema labarai na hukumar Abdulsalam Attiyoh ya sanar da cewa, za'a kammala rajistan a ranar 26 ga watan da muke ciki na Oktoba.
Ofishin MDD a Libya ya yi maraba da kokarin da mahukuntan Libyan ke yi, duk da matsin lamba da suke fuskanta a bangarorin siyasa da tsaro. Sai dai matsalar katin shaidar 'dan kasa ta kawo jinkirin majalissar dokokin kasar ta tabbatar da cikakkun ranakun aiwatar da zabe. (Fatimah)