Ministan harkoki cikin gidan kasar Libya Mohamed Al-Sheikh ya yi murabus a ranar Lahadi daga kan mukaminsa watanni uku kacal bayan nadinsa, a wata sanarwa da hukumomin kasar suka bayar a birnin Tripoli.
Faraministan kasar Ali Zeihan ya karbi wannan murabus na ministan harkoki cikin gida, sannan kuma ya bukaci mataimakinsa mista Al-Seddik Abdelkrim da ya maye gurbin wannan kujera ta ministan cikin gida kafin a nada wani sabo, in ji wannan sanarwa.
Mista Sheikh ya gabatar da wannan murabus nasa ba tare da ba da wani dalili ba.
An nada shi wannan kujera ta ministan harkoki cikin gida a cikin watan Mayu domin maye gurbin Achour Chwayed wanda ya ajiye takarda dalilin korafe korafen da aka rika yi masa na kasawarsa wajen horar da jami'an tsaro.
Kasar Libya dai na fama da rashin tsaro, kamar sauran yawancin kasashen Larabawa dalilin tashen-tashen hankali na siyasa da kuma hare-haren ta'adanci. (Maman Ada)