in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta sanya kungiyoyin Najeriya biyu cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda
2013-11-14 10:52:16 cri

Babbar mashawarci ga shugaba Obama kan harkokin tsaron cikin gida, da yaki da ta'addanci Lisa Monaco, ta ce, Amurka ta sanya kungiyar Jama'atu Ahlussunna Lidda'awati wal jihad ko Boko Haram, da kungiyar Ansaru, cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda.

Lisa Monaco wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba 13 ga wata, ta kara da cewa, mahukuntan Amurkan sun kuma amince da kakabawa wadannan kungiyoyi biyu takunkumi. A cewarta, an dauki wannan mataki ne domin dakile duk wani yunkuri da kungiyoyin za su yi na samun tallafin kudi daga kasar ta Amurka, baya ga dakatar da duk wata kadara da suka mallaka a bankunan kasar.

Sanarwar ta kara da cewa, hakan na nuna irin goyon baya da Amurka ke baiwa mahukuntan Najeriya, a kokarin da suke yi na yaki da ayyukan ta'addanci, da ma yunkurin kawo karshen matsalolin tsaro dake addabar sassan arewacin kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China