in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun sojin Najeriya na kaddamar da hare-hare kan sansanonin Boko Haram
2013-10-31 09:51:38 cri

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana aniyar ci gaba da kaddamar da hare-hare ta kasa da sama, kan sansanonin kungiyar nan ta Jama'atu Ahlussunna Lidda'awati wal Jihad, da aka fi sani da Boko Haram, a wasu kauyukan dake arewa maso gabashin jahohin Borno da Yobe.

Da yake tabbatar da daukar wannan mataki a ranar Laraba, kakakin rundunar ta 7, laftana kanar Mohammed Dole, ya ce, suna daukar wadannan matakai ne domin dakile shirin magoya bayan kungiyar na shiryawa, tare da kaddamar da hare-hare kan fararen hula, da sauran jami'an tsaro.

Dole ya kara da cewa, a baya bayan nan jami'an rundunar ta 7 sun kaddamar da wani samame a Benisheik, dake karamar hukumar Kaga, harin da sabbaba tarwatsa sansanin 'yan Boko Haram din dake kauyen Goho, a yankin Mainok.

Yayin wannan samame, da dama daga 'ya 'yan wannan kungiya sun rasa rayukansu, baya ga wasu da dama da suka tsere zuwa wani sansanin dake Marguba. Dole ya ce, daga bisani dakarun rundunar sojin sun samu nasarar lalata wannan sansani na Marguba, ko da yake ya ce, kawo yanzu ba a tantance da yawan maharan da suka rasa rayukansu sakamakon samamen jami'an rundunar sojin ba.

Daga nan sai Kanar Dole ya yi kira ga al'ummar yankunan da ake kaddamar da matakan sojin, da su kwantar da hankulansu, yana mai cewa, tuni aka sanar da jami'an tsaron yankunan halin da ake ciki, domin daukar matakan kare lafiyar fararen hula. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China