Shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan ya kawar da wani matakin biyan diyya ga mutanen da hare-haren Boko Haram suka rutsa da su wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar dubayan jama'a tun lokacin da kungiyar ta kishin islama ta fara kai hare-hare a cikin wannan kasa dake yammacin Afrika.
Amma duk da haka, gwamnatin Najeriya za ta yi iyakacin kokarinta domin taimakawa mutanen da wannan rikici ya rutsa da su ta wasu fannoni, in ji shugaba Jonathan a Abuja a yayin da yake karbar rahoton kwamitin sasantawa da warware matsalolin tsaro a arewacin Najeriya.
Gwamnati ba za ta biyan diyya ba, ba wai batun biyan diyya ba ne, amma maganar ita ce ta wace hanya da za mu iyar taimakawa mutanen farfado wa da kansu bisa wannan magana da gwamnati take mai da hankali a halin yanzu, in ji shugaban tarayyar Najeriya. (Maman Ada)