in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 40 suka mutu sakamakon hare-haren da aka kai musu a kauyukan Nigeriya
2013-11-05 10:13:17 cri

Kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya samo mana labarin cewa, akalla mutane 40 ne aka tabbatar da rasa rayukansu sakamakon hare-haren da wassu mutane masu dauke da makamai da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai musu a kauyuka biyu dake jihar Borno a arewacin kasar Nigeriya.

A kauyen Gulumba dake arewa maso gabashin jihar ta Borno, mutane 27 ne aka harbe har lahira, guda 12 suka ji rauni, sannan aka saka wa gidaje 300 wuta a lokacin wannan harin da 'yan bindigar suka kai a ranar Alhamis din da ta gabata kamar yadda shugaban karamar hukumar Bama Alhaji Baba Shehu Gulumba ya shaida wa manema labarai.

Ya koka da cewar, rashin hanyar sadarwa mai kyau dalilin tsaro da gwamnati ta kafa a jihar, shi ya kawo jinkirin sanar da jama'a labarin harin cikin lokaci.

A cewar Alhaji Baba Shehu Gulumba, maharan sun kai harin ne a kan Babura, wassu kuma a cikin motar a kori kura suna ta harbin kan mai uwa da wabi.

A wani harin na daban kuma a safiyar ranar Asabar din da ta gabata, jami'an gwamnati sun tabbatar da cewar, an yi wa wassu mutane 13 kwantar bauna a wata mahada a kan hanyar Banki a jihar.

Su dai wadanda aka hallaka a ranar Asabar din suna cikin wata bas din fasinja ne dake wucewa a kan hanyar, in ji shugaban karamar hukumar ta Bama. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China