in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ceto 'yan bakin haure guda 62 daga hamadar Algeriya
2013-11-06 10:47:13 cri

Sojojin gwamnatin kasar Algeriya suka ceto a kalla 'yan bakin haure 62 da yunwa da kishirwa suka kusa hallaka su, daga hamadar yankin Tamanrasset, a kudu da babban birnin kasar Algiers, kamar yadda wata majiyar tsaro ta tabbatar.

Dakarun sojin kasar ta Algeriya sun hango wadannan 'yan bakin haure ne wadanda galibinsu sun fito daga kasashen Niger da Guinea, inda a nan take suka ba su agajin gaggawa kafin suka garzaya da su asibitin sojoji dake kusa, in ji wannan jami'i wanda bai bayyana ko mutane suna cikin hadari ba bayan hakan ko kuwa a'a.

Jami'in ya yi bayanin cewa, 'yan bakin hauren da sojojin kasar Algeriyan suka yi wa rakiya sun taso ne daga garuruwan Agads dake arewacin jamhuriyar Niger, sun tafi Tamanrasset, sai dai kuma suka kasa kammala tafiyar tasu mai dauke da hadari saboda motocinsu biyu sun lalace gaba daya.

Mutanen da aka ceto sun tabbatar da cewar, wadanda suka yi fataucin su sun watsar da su a tsakiyar Hamada, abin da ya sa suka jure duk yunwar da suke ji da kishirwa, zafi da kuma guguwar hamada mai karfi har na tsawon kwanaki biyar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China