in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da yaki da musugan haurin giwa
2013-11-05 20:54:53 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya fada yayin taron manema labarai a yau Talata cewa, kasar Sin ta bayyana kakara cewa, ba ta goyon bayan sumugan haurin-giwa kuma za ta ci gaba da aiki da kasashen duniya wajen kare namun daji.

Hong Lei ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da Sinawan nan 3 da aka kama a kasar Tanzaniya da tarin haurin giwa a gidajensu.

Mr Hong ya ce, kasar Sin tana sa-ido sosai kan batun, kuma tuni jakadan kasar Sin da ke kasar Tanzaniya ya nazarci bayanan tare da bayar da sanarwa mai karfi ta yin allawadai da yadda ake farautar dabbobi da sumugan haurin-giwa tare da alkawarin yin hadin gwiwa a yaki da munanan ayyuka.

Ya kuma bayyana cewa, ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar ta Tanzaniya ya yi kira ga Sinawa masu yawon shakatawa da su kasance masu mutunta dokokin kasar, kana su guji yin sumugan haurin-giwa.

Mr Hong ya kuma bukaci 'yan sandan kasar Tanzaniya da su rika daukar matakai kamar yadda doka ta tanada, kana su kare 'yancin Sinawa bisa doka.

Ya kuma jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin ko kadan ba ta goyon bayan farautar giwaye da sumugan haurin-giwa, kuma ta dauki matakan da suka dace, ciki har da sanya doka, hade dokokin da suka dace da yin hadin gwiwa da kasasahen duniya wadanda suka taimaka wajen hana cinikin haurin-giwa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China