An bayyana kungiyar tarayyar Afirka ta AU a matsayin wadda za ta yanke hukunci, game da batun yiwuwar ci gaba da kawancen kasashen Afirka, da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ko ICC a takaice.
Ministar ma'aikatar huldar kasa da kasa ta Afirka ta Kudu, uwar gida Maite Nkoana-Mashabane ce ta bayyana hakan ga manema labaru a birnin Pritoria dake kasar ta Afirka ta Kudu. Nkoana-Mashabane ta kara da cewa, Afirka ta Kudu za ta ci gaba da kasancewa mai nuna cikakken goyon bayanta, ga shawarar da kungiyar ta AU za ta yanke kan wannan batu.
Wannan dai tsokaci na ministar Nkoana-Mashabane, na zuwa ne gabanin wani taron gaggawa da AU za ta gudanar a ranekun 11 da 12 ga watan nan a birnin Addis Ababa na kasar Habasha. Ana sa ran taron na wannan karo zai ba da damar yanke hukunci kan ko AU, za ta ci gaba da goyon bayan kotun ta ICC ko kuwa a'a.
A baya bayan nan dai wasu kasashen Afirka sun yi barazanar janye goyon bayansu ga kotun ta ICC, sakamakon zargin ta da suka yi na nuna banbanci, tare da kafawa shuwagabannin nahiyar ta Afirka kahon zuka.
Wannan dai zargi baya rasa nasaba da fara shari'ar shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, da mataimakinsa William Ruto da kotun ta yi, bisa zarginsu da aikata laifuka masu alaka da ingiza jama'a su tada tarzoma, yayin babban zaben kasar na shekarar 2007, lamarin da ya haddasa kisan mutane sama da 1,000.
Kotun ta ICC wadda aka kafa a shekarar 2002, karkashin yarjejeniyar birnin Rome, na da nauyin hukunta laifukan yaki, da na keta hakkokin bil'adama, tana kuma da kasashe mambobi 122, inda 34 daga cikinsu suka fito daga nahiyar Afirka. (Saminu)