Minista a ma'aikatar shari'ar kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya soki lamirin kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC, yana mai bayyana ta da cewa, kotu ce dake nuna wariya, tare da kokarin muzgunawa shuwagabannin Afirka kadai.
A ganinsa, ya dace kotun ta tuhumi tsoffin shuwagabanni irin su George Bush na Amurka, da tsohon firaministan Birianiya Tony Blair, bisa irin rawar da suka taka a yakin da kasashensu suka gudanar a Iraqi.
Mnangagwa ya kara da cewa, lokaci ya yi da mahukuntan nahiyar Afirka, za su tashi tsaye wajen daukar matakin dakile wannan halayya da ICC ke nunawa. Tsokacin nasa dai na zuwa ne gabanin taron kungiyar tarayyar Afirka ta AU, wanda aka shirya gudanarwa a karshen makon nan, taron da ake fatan zai tattauna matsayin kasahen nahiyar dangane da dorewar goyon bayansu ga ICC ko akasin hakan.
Dama dai a baya ma kungiyar AU ta taba zargin ICC da matsin lamba ga shugabannin da suka fito daga Afirka, tare da kyale wasu shuwagabannin yammacin duniya, da AU ke ganin ya dace a tuhuma bisa laifukan yaki da suka aikata.
Kotun ICC dai na da kasashe mambobin ta 122, ciki 34 sun fito ne daga nahiyar Afirka. (Saminu)