in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da UNESCO sun kaddamar da wani shirin cike gibin rashin ingancin ba da ilmi a Afrika
2012-11-23 10:15:45 cri

Bisa manufar hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa ta UNESCO da kuma taimakon kasar Sin ne, aka kaddamar a ranar Alhamis a cibiyar UNESCO da wani shiri na shekaru hudu masu zuwa domin cike gibin rashin ingancin ba da ilmi a Afrika.

Shi dai wannan shiri na da manufar gaggauta samun cigaba wajen cimma maradun samun ilmi ga kowa da kuma maradun cigaba na sabon karni da suke da nasaba da horo, da mai da hankali ga kyautata tsare-tsaren horar da malaman makaranta, bisa hangen nesa da ya shafi horar da wani adadi mai yawa na kwararrun malaman makaranta a Afrika.

Kasashen Afrika takwas za su sami wannan gajiya, uku daga cikinsu za su samu moriyar wannan shiri tun daga shekarar farko, kasashen sun hada da Cote d'Ivoire, Habasha da Namibia. Kana sauran kasashe biyar za'a zabe su ta la'akari da tsarin aikin UNESCO a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara da siyasar bunkasa dangantakar cigaba ta kasar Sin, musammun a kasashen da kakorinsu ya ja da baya a fannin ba da ilmi, dalilin karancin malaman makaranta.

A cikin jawabinsa na kaddamar da wannan shiri, zaunanan wakilin kasar Cote d'Ivoire a UNESCO, mista Denise Houphouet-Boigny ya nuna godiya ta musammun ga gwamnatin kasar Sin bisa taimako da mai da hankalin da take a nahiyar Afrika. Kuma wannan taimako na kasar Sin ya zo a lokacin da ake bukatarsa domin zai taimaka wajen fara horar da malaman makaranta. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China