in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
M23 dake DRC na shirin aje makamai bayan shan kaye daga dakarun gwamnati
2013-11-06 10:35:22 cri

Kungiyar 'yan tawaye na M23 na kasar jamhuriyar DRC a ranar Talatan nan suka nuna shirinsu na aje makamai bayan koma bayan da suke ta fuskanta a cikin makonnin da suka gabata.

Shugaban kungiyar Bertrand Bisimwa ya nuna a cikin wata sanarwa cewa, an shawarci dakarunsa da su aje makamai domin shirin mika wuya a cikin wani kokarin cimma matsaya tare da gwamnatin.

Kungiyar 'yan tawayen wadda ita ce mafi girma a kasar dake tsakiyar nahiyar Afrika sun yi watsi da sansaninsu dake kan tsaunuka a kan iyaka da kasar Uganda da Rwanda, in ji sojojin kasar a ranar Talata. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China