in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun gwamnatin Congo sun yi ikirarin tunbuke saiwar kungiyar M23
2013-10-31 10:57:58 cri

Rundunar dakarun sojin gwamnatin jamhuriyar dimokaradiyar Congo FARDC, ta sanar da kammala yaki da kungiyar dakarun nan masu dauke da makamai ta M23, bayan da ta samu nasarar tarwatsa matattarar dakarun dake lardin Arewacin Kivu.

Mai magana da yawun fadar gwamnatin kasar Lambert Mende ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, yana mai cewa, dakarun gwamnatin sun kame garin Bunagana, wanda ke kan iyaka da Uganda, lamarin da ya tilastawa jagoran M23 Bertrand Bisimwa tserewa zuwa kasar Ugandan.

Don haka ne ma Mende, ya yi kira da kasar Uganda, dake matsayin mai shiga tsakani a zaman tattaunawar da mahukuntan Congo, da wakilan 'yan tawayen ke yi, da ta mika Bisimwa gida domin fuskantar hukunci.

Kame garin Bunagana dai ya zo ne bayan da a ranar Juma'ar makon jiya, dakarun gwamnatin na FARDC, da majalisar dinkin duniya ke mara wa baya, suka fatattaki 'yan tawayen kungiyar ta M23 daga matattararsu dake Kibumba, mai nisan kilomita 23 daga hedkwatar kasar wato Goma.

Har ila yau kakakin rundunar ta FARDC dake yankin Arewacin Kivu Olivier Hamuli, ya yi alkawarin 'yantar da daukacin yankunan da kungiyar ta M23 ke iko da su, bayan samun nasarar kwace garin na Bunagana.

Rahotanni dai sun bayyana rikicin cikin gida da kungiyar ta M23 ta fuskanta cikin watan Maris da ya gabata, a matsayin musabbabin raguwar karfinta. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China