in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake bude taron shawarwari tsakanin gwamnatin DRC da wakilan kungiyar M23
2013-09-11 10:35:21 cri

Rahotanni daga Kampala, babban birnin kasar Uganda na nuna cewa, wakilan gwamnatin jamhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC, da na kungiyar 'yan tawayen M23 sun fara tattaunawa, domin lalubo bakin zaren matsalolin siyasar kasar ta Congo wadda ya ki ci ya ki cinyewa.

A wannan karo dai ana sa ran shawarwarin da aka fara gudanarwa a ranar Talata 10 ga wata, za su ba da damar dakatar da fadace-fadace dake addabar yankin gabashin kasar mai arzikin ma'adanai.

Da yake karin haske don gane da yanayin gudanar wannan taro, jami'i mai shiga tsakani, kuma ministan tsaron kasar Uganda Crispus Kiyonga, ya bayyanawa manema labarai cewa, sassan biyu na mai da hankali ga nazartar daftarin wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa, wanda ake fatan zai ba da damar warware banbance-banbancen dake tsakaninsu nan da makwanni biyu masu zuwa.

Kiyonga, ya kuma bayyana takaicinsa don gane da yadda fadace-fadacen baya bayan nan a kasar ta Congo suka janyo asarar rayuka masu yawa, yana mai fatan cewa, ba za a sake samun barkewar rikici yayin da ake tsaka da tattaunawar ba.

Bugu da kari minsitan tsaron kasar ta Uganda ya yi kira da bangarorin dake tattaunawar da su kai zuciya nesa, domin ba da damar cimma daidaito cikin lumana.

Shawarwarin da aka fara gudanarwa na wannan karo dai sun biyo bayan umarnin da shuwagabannin yankin Greak Lakes suka bayar ne, na gaggauta fara tattaunawa cikin makwanni biyu. Kuma ko da yake an sanya ranar Litinin ta zamo ranar farko ta fara taron, da dama daga wakilai ba su isa birnin na Kampala a kan lokaci ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China