Kakakin MDD Farhan Haq, ya ce, sabon fada da ya barke a karshen makon da ya gabata, tsakanin dakarun sojin jamhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC da na 'yan tawayen M23, ya yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama, tare da haddasa yanayin zaman dar dar tsakankanin al'ummar kasar.
A cewar Haq, mayakan kungiyar M23 sun yi amfani da manyan bindigogi wajen kai hare-hare a yankuna masu yawan al'umma. Cikin wuraren da suka fuskanci hare-haren na ranar Asabar, hadda yankin Ndosho dake birnin Goma, harin da ya haddasa rasuwar mutum guda, tare da raunata wasu mutane 5.
Rahotanni daga birnin na Goma dai na cewa, kashe wani farar hula da dakarun 'yan tawayen M23 suka yi a Goma ne, ya haddasa barkewar tarzoma a sassan birnin. An kuma ce, masu zanga-zanga sun yi kokarin kutsa kai cikin sansanin MDD dake kusa da filin tashi da saukar jiragen saman Goma, inda kuma yunkurin rundunar wanzar da zaman lafiya ta MONUSCO na shiga tsakani, ya janyo rasuwar mutane 2, tare da jikkatar wasu mutane 6.
Da yake karin haske don gane da matakan da tawagar ta MDD ke dauka a wannan yanayi, Haq, ya ce, majalissar da hadin gwiwar rundunar sojin kasar, na gudanar da bincike kan dalilan aukuwar tarzomar, baya ga yunkurin kiyaye rayukan fararen hula daga hare-haren kungiyar 'yan tawaye ta M23. (Saminu)