Yayin da yake ganawa da firaministan gwamnatin wucin gadi ta kasar Guinea-Bissau Rui Duarte de Barros, Wang Yang ya bayyana cewa, Sin tana kokarin raya dangantakar hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasar Guinea-Bissau, kana za ta ci gaba da nuna goyon baya ga Guinea-Bissau wajen samun zaman lafiya da bunkasuwa, kuma yana fatan kasashen biyu za su kara yin hadin gwiwa a fannonin aikin noma, kamun kifi, ma'adinai, albarkatun ma'aikata da dai sauransu.
A nasa bangare, Barros ya bayyana cewa, kasarsa tana son zurfafa dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, da kara yin hadin gwiwa a fannoni daban daban, ta yadda za a raya kasar yadda ya kamata.
Za a gudanar taron ministoci karo na 4 na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da kasashe masu amfani da harshen Portugese a ranar 5 ga wata a yankin Macau. Ana sa ran Wang Yang zai halarci bikin bude taron tare da yin jawabi. (Zainab)