in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci mambobin kasashen MDD da su magance matsalar nuna bambanci wajen samun abubuwan more rayuwa
2013-10-31 10:36:05 cri

A ranar Laraba ne galibin hukumomin MDD suka yi kira ga kasashe mambobinta, da su dauki matakan da suka dace don tabbatar da cewa, manufofin samun ci gaba bayan shekarar 2015 da ake kokarin fitarwa, za su magance matsalar nan ta rashin daidaito da miliyoyin mutane ke fuskanta na samun muhimman kayayyakin more rayuwa.

A cikin sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, asusun tallafawa yara na MDD (UNICEF), ofishin babban kwamishinan kare hakkin bil-adam (OHCHR), hukumar samar da ruwa mai tsafta da hukumar musamman mai kula da kare hakkin bil-adam kan samar da ruwan sha da tsaftar muhalli, suka bukaci mambobin kasashe, da su tsara sabbin manufofin ba tare da nuna wani bambanci ba.

An fitar da wannan sanarwar ce gabanin taron tattaunawar da za a yi a hedkwatar MDD da ke birnin New York, kan samar da daidaito a manufofin ci gaban da ake son samarwa bayan shekarar 2015, wani sabon mataki na samar da ruwa da tsaftace muhalli ga kowa (WASH) wadda tawagar din-din-din ta MDD da ke kasar Finland da ofishin musamnan na Majalisar suka shirya tare.

Sanarwar ta ce, wannan shi ne darasi mai muhimmanci da aka koya karkashin shirin nan na muradun karni (MDGs) wanda ke kunshe da wasu hanyoyin yaki da talauci guda 8, wato samar da ilimi, nuna daidaiton jinsin, lafiyar mata da kananan yara, kiyaye muhalli, rage cutar kanjamau da hadin gwiwar kasa da kasa don samar da ci gaba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China