in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi allawadai da batun shirya zaben raba gardama a Abyei
2013-10-29 10:31:51 cri

Kungiyar tarayyar Afrika AU ta yi allawadai da babbar murya kan shirya zaben raba gardama a Abyei, yankin da yanzu haka yake a karkashin mulkin kasar Sudan da kuma kasar Sudan ta Kudu take ikirarin nata ne.

Ta bakin wani kwamitin manyan jami'ai na (AUHIP), kungiyar AU na cigaba da ba da kokarinta na sasantawa tsakanin kasar Sudan da Sudan ta Kudu domin taimaka wa kasashen biyu dake makwabtaka da juna warware wasu matsalolinsu dake kan tebur. Kungiyar AU ta ba da wata sanarwa a ranar Litinin dake bayyana cewa, shugabar kwamitin kungiyar AU, madam Nkosazana Dlamini-Zuma tana sanya ido sosai kan halin da ake ciki a yankin Abyei. Shugabar ta damu sosai kan labarin wani zaben jin ra'ayin jama'a da shugabannin al'ummar Ngok Dinka suke shirin shiryawa domin tabbatar da matsayin karshe na Abyei.

Madam Dlamini-Zuma ta fahimci bacin ran jama'a na ganin cewa, zaben raba gardamar bisa yarjejeniyar zaman lafiya, an kasa shirya shi, amma kuma, a cewar jami'ar, wannan ba hujja ba ce ta daukar wani mataki, domin mataki ne na rashin da'a wanda ba'a amince da shi ba, in ji wannan sanarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China