in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya yi matukar Allah wadai da kisan jami'an wanzar da zaman lafiya a Abyei
2013-05-07 12:28:39 cri

Kwamitin tsaron MDD ya yi matukar Allah wadai da kisan wasu jami'an wanzar da zaman lafiya, ranar Asabar din makon da ya gabata a yankin Abyei mai arzikin man-fetir, yankin da kasashen Sudan da Sudan ta Kudu ke takaddama a kansa.

Wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin 6 ga watan ta bayyana amincewar da Sudan ta yi da batun gudanar da sahihin bincike, tare da alkawarin hukunta wadanda aka samu da laifi, a matsayin wani abin a yaba. Har ila yau, kwamitin tsaron ya jinjinawa alkawarin da Sudan ta Kudu ta yi na ci gaba da nuna goyon baya ga tawagar UNISFA.

Rahotanni sun bayyana cewa, harin na ranar Asabar, wanda dakarun Misseriya suka kaiwa tawagar UNISFA, ya sabbaba kisan babban jagoran al'ummar Ngok Dinka mai suna Dengkuol Deng, tare da wani jami'in tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD, 'dan asalin kasar Habasha, baya ga wasu abokan aikinsa biyu da aka ce su ma sun samu munanan raunuka. Kabilar Ngok Dinka dai reshe ce ta kabilar Dinka, wadda ita ce kabila mafi girma a dukkanin fadin kasar Sudan ta Kudu

MDD ce dai ta baiwa tawagar UNISFA ikon gudanar da ayyukanta tun cikin watan Nuwambar bara, tana kuma kunshe da dakarun soji 4200, da 'yan sanda 50 tare da wasu fararen hula da dama. Bisa yanayin da ake ciki, tawagar ta bukaci a dauki matakan aiwatar da yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka cimma a baya, tare da zage dantse wajen zakulo hanyoyin warware batutuwan da ake takaddama a kansu, ciki hadda fidda matsayin karshe ga yankin na Abyei.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China