in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu ta yi kira ga Sudan da ta amince da shawarar AU kan batun Abyei
2013-09-04 10:30:37 cri

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit ya yi kira a ranar Talata ga kasar Sudan da ta amince da shawarar kungiyar tarayyar Afrika AU game da zancen shirya zaben raba gardama kan wannan yanki mai arzikin man fetur na Abyei, a yayin shi kuma shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir yake jaddada cewa, yin shawarwari ita ce sahihiyar hanyar warware wannan rikici. 'A nawa ra'ayi, batun yankin Abyei an warware shi. Mun warware wannan matsala bisa tsarin cimma sulhu da fahimtar juna na CPA bisa taimakon yarjejeniyar Abyei.' in ji mista Kiir a yayin bikin bude taron tattaunawar hadin gwiwa tare da takwaransa na kasar Sudan a birnin Khartoum.

A nasa bangare, mista Al-Bashir ya yi alkawarin cigaba da yin shawarwari domin bullo da wata hanyar magance matsalar Abyei, game kuma da sauran batutuwa dake kan tebur, musammun ma batun Abyei, ya ce, muna bukatar kara jaddada niyyarmu ta cimma bakin zaren wannan matsala baki daya da dukkan bangarorin da abin ya shafa za su amincewa. Daga karshe shugaban kasar Sudan ya jaddada muhimmancin kafa hukumomin wucin gadi na fararen hula a yankin Abyei. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China