Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya yi allawadai da babbar murya a ranar Laraba game da wani harin kunar bakin wake da aka kai wa sojojin rundunar kasa da kasa ta MDD kan tabbatar da zaman lafiya a kasar Mali ta MINUSMA.
Wasu maharan da suka boye kamaninsu sun afkwa wata tashar bincike ta sojojin MINUSMA dake garin Tessalit, inda suka kashe da jikkata sojojin kasar Chadi dake cikin wannan tawaga. Haka kuma akwai fararen hula da dama da wannan hari ya rutsa da su, in ji kakakin Ban Ki-moon.
Wannan hari ba zai karya lagon kokarin MDD ba wajen taimakawa maido da tsaro, kwanciyar hankali da zaman lafiya cikin karko a kasar Mali dake yammacin nahiyar Afrika, in ji wannan jami'i tare da isar da ta'aziyyar mista Ban ga iyalan mutanen da harin ya rutsa da su. (Maman Ada)