Bisa yunkurin fadada tsarin samar da wutar lantarki tsakanin Mali da Guinee, kwararrru daga wadannan kasashe biyu sun bude wani zaman taro na kwanaki biyu a ranar Talata a birnin Bamako domin amincewa da wani rahoton bincike kan yiyuwar kafa cibiyoyi biyu na musamman. Bincike na yiyuwar wannan shiri ya samu tallafin kudi Sefa biliyan biyu daga bankin cigaban Afrika. Bisa rahoton da aka gabatar domin samun amincewa, Franck Aly Keita, ministan makamashi da ruwa na kasar Mali ya bayyana cewa, rahoto na cikin tsarin neman zuba jari ga wannan shiri. 'Hakika, tanadi kudade ba zai isa ba, dole sai an yi bincike ta fuskar kimiyya, tattalin arziki, kudi da manufar cigaba mai karko.' in ji mista Keita.
Bisa amfanin wannan aiki samar da wutar lantarki tsakanin kasashen biyu, Mohamed Bah, jagoran shirin a bangaren kasar Guinee ya nuna cewa, aikin zai kawo kasashen biyu babbar riba ta fuskar wutar lantarki, musammun ma ga kasar Guinee dake da arzikin ruwa.
Hada layin wutar lantarkin tsakanin kasashen biyu ya shafi tsawon kilomita 920 wanda a ciki Mali na da kilomita 300. (Maman Ada)