in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci taimakon abinci ga arewacin Mali
2013-09-24 10:52:36 cri

MDD da abokan huldarta a ranar Litinin din nan suka yi kira cikin gaggawa ta bukatar samar da taimakon abinci ga arewacin Mali, inda gidaje uku a cikin hudu ba su da abin da za su ci a rana saboda tsananin karancin abinci da ake fama da shi a yankin.

Wani bincike na gaggawa da aka gudanar da shi cikin hadin gwiwwa tsakanin gwamnatin Malin da hukumar samar da abinci da aikin noma ta MDD, da hukumar samar da taimakon abinci ta duniya da wassu cibiyoyi 15 dake hadin gwiwwa da MDD, ya kiyasta cewa, kusan mutane miliyan 1.3 ne suke cikin wani mawuyacin hali a yankin inda ba a samu farfadowa ba tun bayan yakin da aka gwabza cikin watannin da suka gabata da kuma karancin abinci a shekarar bara.

Jami'an MDD sun sanar cewar, mutanen da suka rasa muhallinsu da kuma 'yan gudun hijira sun fara koma wa gidajensu, sai dai 'dan abin da ake da shi ba zai ishe su ba, sannan akwai alamun mutanen dake da bukatar taimakon za su karu.

A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwwa da aka fitar wa manema labarai, jami'an sun lura cewa, rashin dabbobi ya kara kawo tasiri ga samar da abinci da kuma rayuwar yawancin mutanen wurin. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China