in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin bam ya hallaka mutane biyu a arewacin Mali
2013-09-29 09:32:34 cri

Wasu 'yan kunar-bakin-wake sun tada bama-bamai da suka dana a jikin wata mota da suke ciki, a kusa da sansanin sojin Cheick Sidi El Bakaye, dake birnin Timbuktu a arewacin kasar Mali.

Majiyar rundunar sojin kasar ta Mali ta shaida wa kamfanin dillancin labarum kasar Sin Xinhua cewa, maharan su uku, na cikin motar a lokacin da ababen fashewar suka tashi, wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwar wasu fararen hula su biyu, baya ga sojoji 4 da suka jakkata.

Wasu mazauna birnin na Timbuktu, sun bayyanawa majiyarmu cewa, akwai yiwuwar samun sojojin da suka rasu sakamakon wannan hari, kasancewar jami'an soji da dama dake tsaron kofar shiga sansanin, har ila yau wani sashi na gidan yarin sojin dake cikin sansanin ya rushe yayin tashin bama-baman. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China