in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Mali zai halarci babban taron MDD karo na 68 a New York
2013-09-23 14:16:52 cri

Shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubar Keita zai isa cibiyar MDD da ke birnin New York na kasar Amurka domin halartar babban taron kungiyar karo na 68, a wani labarin da ya fito daga fadar shugaban kasar Mali a ranar Lahadi.

Taken zaman taron karo na 68 na wannan shekara da za a bude ranar yau Litinin shi ne 'hanyar da za'a bi' wato wani tsarin cigaba game da batun nakasassu zuwa shekara ta 2015.

Wannan taron manyan jami'ai na MDD kan batun nakasassu da cigaba zai gudana ranar 23 ga watan Satumba a birinin New York.

Ziyarar shugaban kasar Mali ita ce ta farkon tun bayan rantsuwar kama aikinsa a matsayin shugaban kasar Mali a ranar 4 ga watan Satumban da muke ciki.

Haka zalika, a yayin wannan zaman taro, batun tura sojojin Afrika a kasar Afrika ta Tsakiya, kasar dake fama da rikici zai kasance kan teburin taron, in ji shugaban kasar Faransa Francois Hollande a yayin da ya halarci bikin rantsar da shugaban kasar Mali a birnin Bamako a ranar Alhamis da ta wuce. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China