in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar fararen hula a Arewacin Kivu ta yi allawadai da harbar M23 kan jirgin saman MONUSCO
2013-10-14 10:58:07 cri

Kungiyar fararen hula dake jihar Arewacin Kivu ta demokuradiyar jamhuriyar Congo DRC ta yi allawadai da babbar murya a ranar Lahadi kan harbe-harben roka da 'yan tawayen M23 suka yi kan wani jirgin sama mai saukar ungulu na tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar wato MONUSCO a yankin Rumangabo mai tarazarar kilomita 98 da arewacin birnin Goma.

A cewar kungiyar fararen hula, wadannan harbe-harbe na 'yan tawayen M23 suna bayyana gaskiyar magana cewa, 'yan tawayen M23 ba su da niyyar ajiye makamai da girmama yarjejeniyar zaman lafiya ta Kampala tsakanin M23 da gwamnatin DRC.

Bisa yin wannan harbi ba tare da yin wani tunani ba kan helikwabtan MONUSCO, 'yan tawayen M23 sun bayyana niyyarsu ta bajirewa gamayyar kasa da kasa da ta taimaka da kawo goyon baya ga yarjejeniyar cimma masalaha da aka tattaba wa hannu a birnin Addis Ababa a ranar Lahadi 24 ga watan Fabrairun shekarar 2010. Mayakan M23 sun nuna cewa, ba shirye suke ba wajen dawo da zaman lafiya a gabashin kasar, in ji mista Medard Hamisi na kungiyar fararen hula ta Arewacin Kivu.

A cikin wata sanarwa ta ranar Juma'ar da ta gabata, manzon musammun na MDD kan yankin Grands Lacs, madam Mary Robinson ta ce, ba za'a rufe ido ba kan harbe-harben dakarun 'yan tawayen M23 kan jirgin sama mai saukar ungulu na tawagar MONUSCO dake kasar RDC-Congo ba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China