Wakilai na sassa masu ruwa da tsaki na ci gaba da hallara a birnin Kampala na kasar Uganda, domin fara taron tattaunawa da aka shirya da nufin warware matsalolin siyasar jamhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC wanda ya ki ci ya ki cinyewa.
Kakakin fadar gwamnatin kasar Uganda Ofwono Opondo ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin 9 ga wata. Opondo ya ce, tuni wakilai daga tsagin gwamnatin Congo, da na kunigyar 'yan tawayen M23 suka fara hallara domin taron da ake fatan zai kawo karshen kiki-kaka dake tsakanin bangarorin biyu.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai jagororin yankin suka gudanar da wani taron gaggawa, suka kuma ba da umarnin bude taron gudanar da sabbin shawarwari tun daga ranar Litinin 9 ga wata, ya zuwa makwanni biyu dake tafe.
A makwannin baya bayan nan, fadace-fadace tsakanin dakarun gwamnatin kasar ta Congo, da na 'yan tawaye na kara tsananta, musamman a gabashin kasar, yayin da kuma dakarun MDD da aka tura kasar ke kokarin fatattakar kungiyoyin 'yan tada kayar baya dake wannan yanki, ciki hadda sansanin dakarun 'yan tawayen M23.
Kasar Uganda ce dai ke ci gaba da shiga tsakani a tattaunawar da ake gudanarwa lokaci bayan lokaci, tun daga watan Disambar shekarar da ta gabata kawo yau. (Saminu)