A ranar Jumma'a 11 ga wata ne wani mutum guda ya mutu, yayin da dubban magoya bayan jam'iyyar 'yan uwa musulmai MB suka yi maci a titunan manyan biranen kasar Masar, don murnar cika kwanaki 100, da sojoji suka hambarar da shugaba Mohammed Morsi daga mukaminsa.
A cewar kamfanin dillancin labarai na kasar ta Masar MENA, wani karin mutum guda ya mutu a yankin Sharqiya, yayin da wasu mutane 7 suka jikkata yayin wata arangama a yankin Damietta.
Sai dai a yankin arewacin birnin Iskandariya kuwa, dakarun tsaro ne suka harba barkonon tsohuwa don tarwatsa wata rigimar daka kaure tsakanin masu goyon baya da masu adawa da Morsi. Kana a birnin Alkahira, an tura sojoji da 'yan sanda ne zuwa dandalin Tahriri, inda jami'an tsaro suka hana masu zanga-zanga isa dandalin Rabba el-Adawya da fadar Quba.
A yankin kudancin Aswan kuwa, jami'an tsaro ne suka kame magoya bayan Morsi guda 5, bayan sun yi musayar wuta da jami'an tsaro. (Ibrahim)