in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana sun yi hasashen karuwar tattalin arzikin nahiyar Afirka
2013-09-27 14:08:26 cri

Wata cibiyar kwararru a fannin tattalin arziki mai suna African Economic Outlook ko AEO a takaice, ta fidda wani rahoto dake hasashen irin ci gaban da kasashen dake nahiyar Afirka ka iya samu tsakanin shekarun 2013 zuwa 2014 mai zuwa.

Rahoton da AEO ta fitar jiya Alhamis, ya nuna cewa, a bana, kasashen dake nahiyar za su samu habakar tattalin arziki da kimanin kaso 4.8 bisa ma'aunin GDP. Har ila yau, wadannan kasashe za su samu karuwa da kaso 5.3 bisa dari a badi bisa ma'aunin na GDP.

Bida kididdigar cibiyar, kasashen dake tsakiyar Afirka za su iya kaiwa ga ci gaban da yawansa ya kai kaso 5.7 bisa dari a shekarar 2013 da muke ciki, da kuma kaso 5.4 bisa dari a shekara mai zuwa. Sai kuma kasashen gabashin Afirka, da hasashen ke cewa na iya samun ci gaba da kaso 5.2 bisa dari a bana, da kuma kaso 5. 6 bisa dari a badi.

Binciken ya kuma nuna yiwuwar kasashen arewacin Afirka su sami kaso 3.9 bisa dari a bana, da kuma kaso 4.3 bisa dari a shekara mai zuwa. Kudanci Afirka kuwa na iya samun karuwa da kaso 4.1 bisa dari a bana, da kuma kaso 4.6 bisa dari a shekarar 2014 dake tafe. Yayin da yankin yammacin Afirka ka iya samun ci gaba da kaso 6.7 bisa dari a bana, da kuma kaso 7.4 a badi.

Cikin jadawalin dake kunshe a wannan rahoto na AEO, kasashen Libya, da Chadi, da Saliyo, da Cote d'Ivoire, da jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Ghana, da Mozambique, da Angola, Zambia, da Ruwanda ne ke kan gaba a hasashen samun ci gaba.

Yayin da kuma kasashen Swaziland, da Equatorial Guinea, da Masar, da Sudan, da Afirka ta Kudu, da Kamaru, da Madagascar, da Algeria, da Lesotho da kuma Seychelles ke matsayin kasashe da hasashen ke cewa, za su samu tsaiko, a fagen ci gaban tattalin arzikinsu, tsakankanin wadannan shekaru biyu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China