Ban da wannan kuma, kakakin Ali Zidan ya tabbatar da wannan labari ga shafin Internet na CNN na Amurka.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, dakarun dauke da makamai da ba a san su wane ne ba, sun yi awon gaba da Zidan a otel da yake zaune, kuma cikin mutanen da aka sace tare da shi, har da wasu na hannun damarsa. Har zuwa yanzu, dai babu wata kungiyar da ta sanar da daukar alhakin wannan lamari.(Bako)