in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakaru masu dauke da makamai sun bukaci a mayar da jami'an gwamnatin Libya saniyar ware a siyasance
2013-04-29 17:09:38 cri

A ranar Lahadi 28 ga wata ne, dakaru masu dauke da manyan makamai sama da 100 suka kai hari tare da kewaya ma'aikatar harkokin waje ta kasar Libya, inda suka bukaci mahukuntan kasar da su zartas da tsarin mayar da wasu jami'an gwamnatin kasar saniyar ware a siyasance.

Wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya ruwaito cewa, motocin yakin dakaru sun toshe titunan dake kewayen ma'aikatar harkokin wajen kasar, kana wasu dakaru sama da guda 10 dauke da bindigogi samfurin AK47 suna sintiri a wurin, lamarin da ya kawo cikas ga zirga-zirgar motoci a wannan yanki.

Kakakin dakarun ya furta cewa, suna bukatar majalisar wakilai da gwamnatin wucin gadi ta Libya da su kau da manyan jami'an da suke da alaka da mulkin Gaddafi, tare da sanar da tarihin aiki na dukkan jami'an diplomasiyyar kasar. Idan ba su sami martani mai gamsarwa kafin ranar 30 ga wata ba, za su dauki karin matakai masu tsanani.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, wasu jami'an da suka yi aiki a gwamnatin Gaddafi su kan karbi cin hanci sosai. A sabili da haka, wasu 'yan majalisar dokoki suka mika bukatar mayar da jami'an gwamnatin kasar saniyar ware a siyasance ga majalisar wakilai, a kokarin kawar da wadannan jami'ai daga sabuwar gwamnatin.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China