Wani mai gabatar da kara na bangaren soji na Libya ya rasu sakamakon kisan gillar da aka yi masa
A ranar 29 Alhamis ne, wani jami'in hukumar tsaron kasar Libya ya bayyana cewa, a wannan rana, an kai harin boma-boman da aka dasa cikin mota a birnin Benghazi da ke yankin gabashin kasar, lamarin da ya haddasa mutuwar wani mai gabatar da kara na bangaren soji na Libya.
Kakakin hukumar tsaro cikin hadin gwiwa ta birnin Benghazi ya bayyana cewa, an kai hari ga mai gabatar da kara na bangaren soji na Libya mai suna Yusuf Alas Fuer, harin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Alas Fuer ya taba shiga aikin yanke hukunci ga manyan jami'an tsohon mulkin Gaddafi da dama na kasar.(Bako)