in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An saka bam a wasu gine-ginen kotu a Bengazhi, inda mutane 13 sun ji rauni
2013-07-29 10:06:44 cri
Gine gine biyu na kotun shari'a a garin Bengazhi dake gabashin kasar Libya a daren ranar lahadin nan aka dasa masu bam suka lalace, abin da ya yi sanadiyyar raunatar mutane 13 kamar yadda majiyar tsaro suka sanar da kamfanin dillanci labarai na Xinhua.

Gidajen shari'ar biyu dai dake da tazarar kilomita daya a tsakanin su wannan ba shi ne na farko ba da aka kai masu hari ne kamar yadda majiyar ta yi bayani.

Mazauna wurin sun ce sunji kara mai karfi daga arewaci da kudancin Bengazhi duka a wannan daren lahadin.

Kwana daya ke nan da fursunoni 1,200 suka tsere daga gidan wakafi na al-kuliya dake Bengazhi amma 'yan sanda da jami'an tsaro sun samu nasarar sake damke wassu. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China