A gun taron majalisar dokokin jama'ar kasar a wannan rana, el-Magariaf ya bayyana cewa, ya girmama wadanda suka gabatar da dokar 'wariyar siyasa' wato cire manyan jami'an da suka yi aiki a lokacin Gaddafi, kana ya zamo kan gaba ta yin murabus don nuna goyon baya ga wannan doka.
Ya ce, ko da yake majalisar dokokin jama'ar kasar tana fuskantar matsaloli da dama a kan aikin kafa doka, amma za ta girmama burin jama'a, ganin cewa idan aka yi amfani da karfin tuwo, zai kai ga lalacewar lamura.
Kakakin majalisar Omar Humaidan ya bayyana a gun taron manema labaru a wannan rana cewa, majalisar za ta jefa kuri'a don zaben sabon shugaban majalisar.
A halin yanzu, mai yiwuwa ne mataimakin shugaban majalisa na farko ko wani wani mataimakin shugaba daban za su maye gurbin el-Magariaf su zama shugaban majalisar na wucin gadi. Idan kuma ba su iya gudanar da ayyukansu yadda ya kamata ba, za a zabi wani dan majalisar mai martaba don zama shugaban wucin gadin.
Majalisar dokokin jama'ar kasar Libya ta zartas da dokar cire manyan jami'an da suka yi aiki a lokacin Gaddafi daga gwamnatin kasar ta yanzu a ranar 5 ga wata. (Zainab)