Rahotanni na nuna cewa, a wata sabuwar arangama a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR, mutane 60 sun rasa rayukansu a karshen makon da ya gabata, duk da tsauraran matakan tsaro da ake dauka tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watannin baya, da yanzu haka ya saka kasar a karkashin gwamnatin wucin gadi na watanni 18.
Sanarwa da ta fito daga ofishin shugaban kasar ta yi bayanin cewa, fadan ya barke ne daga ranar Asabar zuwa Lahadi tsakanin magoya bayan tsohon shugaban kasar da aka hambarar Francois Bozize da tsoffin dakarun 'yan kungiyar Seleka. Kwanaki kadan bayan wata arangama da bangarorin biyun suka yi a Bangui, babban birnin kasar wanda 'yan Selekan suka kai hari kan magoya bayan Bozize domin su kwace masu makamai.
Sanarwar daga ofishin shugaban kasar ta tabbatar da cewa, fiye da mutane 55 ne suka halaka a wannan arangama a yankin Bossangoa, fiye da kilomita 200 daga arewacin Bangui, inda sojoji su kuma suka rasa jami'ansu guda 5.
Kungiyar raya tattalin arziki ta kasashen yankin tsakiyar Afrika ta rigaya ta bayar da wa'adin gwamnatin wucin gadin zuwa watanni 18 wanda ake sa ran gudanar da babban zabe wanda zai kawo karshen wannan fito na fito.
Ma'aikatan wanzar da zaman lafiya a kasar za su karu zuwa 3600 daga 1400 da ake da su yanzu, kamar yadda kwamishinan zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU Ramtane Lamamra ya tabbatar a ranar Jumma'ar da ta gabata. (Fatimah)