in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
EU da Faransa da MDD sun yi kira da a gaggauta gudanar da ayyukan jin kai a CAR
2013-09-26 16:04:13 cri

Wasu manyan jami'an MDD, da na kungiyar tarayyar Turai EU, da kasar Faransa, sun bayyana matukar bukatar da ake da ita, ta daukar matakan shawo kan mawuyacin hali da al'ummar jamhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR ke ciki.

Jami'an sun bayyana bukatar gaggauta samar da shirin ba da agaji ga al'umman da yakin basasar kasar ya ritsa da su, suna masu rokon samar da karin kudaden gudanar da ayyukan jin kai, matakin da a cewarsu zai yi matukar amfani, baya ga kara samar da tsaro, da zai kasance ginshikin isar tallafi ga wadanda tashin hankulan kasar ya fi shafa.

Wannan bukata dai ta biyo bayan ganawar da jami'ar kungiyar EU Kristalina Georgieva, da mataimakin sakatare janar a MDD Valerie Amos, da kuma ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius suka yi, kan rikicin kasar ta Afirka ta Tsakiya, gabanin mahawarar da mahalarta babban taron MDDr za su yi kan batun.

Daukacin jami'an dai sun amince da kasancewar rikicin kasar a matsayin wata babbar masifa, da ta mamaye dukkanin al'ummar kasar su sama da miliyan 4.6. Rahotanni sun bayyana cewa, a 'yan makwannin nan yawan wadanda suka rasa matsugunnansu, sakamakon fadace-fadacen dake wakana a kasar sun kai mutune 400,000. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China