in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kusan mutane 100 suka mutu a wani fada a CAR
2013-09-12 10:18:45 cri

Rahotanni daga Bangui a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR na nuna cewa, kusan mutane 100 ne suka halaka a kwanakin da aka kwashe ana tabka fada tsakanin magoya bayan hambararren shugaban kasar Francois Bozize da kuma na shugaba mai rikon kwarya na yanzu Michel Djotodia, kamar yadda gidan rediyon kasar ta tabbatar.

A cikin wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban kasar, an ce, fadan ya barke ne tun ranar Asabar, abin da ya shafi mutane fiye da 150, a cikin su, 100 suka mutu, sama da 50 kuma suka ji rauni.

Wuraren da wannan mummunan fada ya fi shafa su ne Bossangoa da Bouca dake arewa maso yammacin Bangui, babban birnin kasar.

Levy Yakete, kakakin tsohon hambararren shugaban kasar a kwannan nan ya ce, wannan hari tsaffin sojoji ne suka kai shi domin su dawo da Bozize a karagar mulki ya karashe wa'adinsa tun da al'umma ne suka zabe shi.

Michel Djotodia dai shi ne ya karbi ragamar mulki a matsayin shugaban rikon kwarya a watan Agusta bayan hambarar da Bozize a watan Maris, abin da kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta kira juyin mulki, sannan kuma kungiyar tarayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS suka ba da wa'adin watanni 18 domin a aiwatar da babban zabe da zai kawo karshen tashin hankali.

Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya dai wadda ta samu 'yancin kai a shekarar 1960 daga renon kasar Faransa ta sha fuskantar juyin mulki sau da dama, kuma yanzu haka an riga an kai ma'aikatan wanzar da zaman lafiya 1400 a kasar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China