in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban AU ya bukaci sabon jadawalin cigaba da zai kula da bukatun Afrika
2013-09-26 10:59:43 cri

Shugaban kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU Hailemariam Dessalegn a jiya Laraba ya yi kiran da a fitar da sabon jadawalin duniya na dogon lokaci da zai dubi abin da ya fi muhimmanci ga cigaban nahiyar bayan shekara ta 2015 wato karewar shirin muradun karni na MDD.

Hailemariam Dessalegn wanda shi ne firaministan kasar Habasha, a cikin jawabinsa wajen babban taron muhawara na majalissar ya ce, al'ummar nahiyar na matukar fatan ganin cewar, kasashen duniya sun fitar da wani sabon jadawali da zai duba muhimman bukatu da za su kawo wa nahiyar cigaba.

Jadawalin cigaban da za a tsara nan da shekaru 50 masu zuwa a nahiyar yana da burin samar da kudurin yaye talauci da inganta ayyukan kawo cigaba mai karko, in ji shi.

Ya ce, wannan karni na 21 zai zama na Afrika idan har aka daidaita kokarin samar da dawwamammen cigaba cikin sauri da zai kyautata tattalin arziki da nahiyar ta dade tana son gani fiye da shekaru 10, don haka ya ce, akwai dalilin da ya sa cigaban Afrika ke matsowa kusa ba da dadewa ba.

Taken taron wannan karon na 68 na majalissar shi ne bayan shirin cigaba na shekarar 2015, tsara wani jadawali mai inganci da zai yaye talauci gaba daya, da sauran abubuwan da ke jawo shi a shekaru masu zuwa bayan kammala shirin muradun karni na shekara ta 2015. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China