Majalissar zartaswar tarayyar Najeriya ta amince da wata yarjejeniyar hadin gwiwa kan batun inganta tsaro, da aka sanyawa hannu tsakanin Najeriyar da jamhuriyar Nijar. Har ila yau majalissar ta amincewa da wata yarjejeniyar fahimtar juna da ta shafi harkar ta tsaro, wadda Najeriyar ta rattabawa hannu tsakaninta da kasar Birtaniya.
Ministan watsa labarun kasar Labaran Maku ne ya tabbatar da hakan, bayan kammala taron majalissar na ranar Laraba 14 ga watan nan, wanda kuma shugaba Goodluck Jonathan ya jagoranta. A cewarsa, an kai ga daukar wannan mataki ne bayan cikakken jawabi da karamin ministan tsaron kasar Erelu Olusola Obada ya gabatarwa majalissar.
Maku ya ce, yarjejeniyar da ta shafi inganta harkar tsaro tsakanin Najeriya da Nijar, na da burin ganin kasashen biyu sun ci moriyar hadin gwiwa don gane da tsaron iyakokinsu, tare da ba da damar fuskantar kalubalen ayyukan ta'addanci da zirga-zirgar bata gari. Har ila yau ministan ya ce, wannan yarjejeniya za ta share fagen musayar dabarun aikin tsaro, da kuma dakile matsalolin karancin tsaron da arewacin kasar ke fuskanta a halin yanzu.
Don gane da yarjejeniyar fahimtar juna da kasar Birtaniya kuwa, ministan watsa labarum, cewa ya yi, hakan zai ba da damar musayar bayanai, da inganta samun horon yaki da ayyukan ta'addanci, wanda bangarorin biyu za su ci gajiyarsa. (Saminu)