A ranar Litinin, gwamnatin kasar Najeriya ta baiyana cewa, kasar ta yammacin Afrika ta kusan kawo karshen kalubalen tsaro da take fuskanta.
Ministan ayyuka na musamman da huldar harkokin gwamnati Kabiru Turaki ya baiyana cewa, matsalar tsaron za ta zo karshe, cikin sanarwar bukin ranar jin kan bil adama na duniya, a birnin Abuja.
Ya bukaci daukacin 'yan Najeriya su ci gaba da ba da muhimman bayanai ga jami'an tsaro tare da cewa, manufar gwamnati ita ce, ba wai ta mai da martani kan hari ba, maimakon hakan, tana nufin hana aukuwar harin ne baki daya.
Ya ce, za'a cimma nasarar hakan ne da hadin kan 'yan Najeriya.
Turaki ya kuma bukaci 'yan Najeriya su tuno da masu ayyukan jin kan bil adama da suka rasa rayukansu a kokarin taimakawa miliyoyin jama' a, a fadin duniya. (Lami)