in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na bukatar dalar Amurka miliyan 244 don kafa na'urar sa ido a kan iyaka
2013-05-24 10:03:09 cri

Ministan harkokin cikin gida na kasar Najeriya Abba Moro ya fadi ranar Alhamis cewa, kasar ta yammacin Afirka na bukatar dalar Amurka miliyan 244 don kafa na'urar sa ido a kan iyakokinta don aikin tsaro.

Da yake jawabi ga kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP mai mulki a kasar a birnin Abuja, ministan ya ce, wani kamfanin kasar Sin ya mika takardar ababan bukata na kafa na'urar.

Ministan na mai cewar, kan iyakokin kasar ba su da cikakken tsaro, don haka, ma'aikatar na bakin kokarinta don shawo kan lamarin.

Ya ce, kafa wannan na'ura wani yunkuri ne a bangaren ma'aikatar wajen yin amfani da fasaha da kuma ma'aikata don a samu cikakken tsaro a kan iyakokin.

Ministan ya ci gaba da cewa, wannan mataki ya zamo wajibi bisa la'akari da karuwar kalubale na tsaro a wasu jihohin arewacin kasar.

Ya kuma bayyana cewa, sashen harkokin wajen kasar Amurka ta yi wa Najeriya tayin ba da tallafi a wannan fuska a matsayin kokarinta na yaki da ta'addanci a kasa da kasa kuma tuni aka fara daukar wasu na'urorin.

Ya ce, da zaran an kammala ayyukan guda biyu, za'a samu tabbatar da tsaro a barayin hanyoyi guda 1,497 da ake amfani da su a shigo kasar. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China