in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A Najeriya wasu hare-hare sun hallaka mutane 85 cikin kwanaki 5
2013-09-30 10:15:47 cri

Rahotannin baya bayan nan daga rundunar sojin tarayyar Najeriya na cewa, kimanin mutane 85 ne suka rasa rayukansu cikin kwanaki 5 a yankunan arewacin kasar. Hakan dai ya biyo bayan irin farmakin da 'yan bindiga da ake zaton magoya bayan kungiyar nan ta Boko Haram ne ke kaddamarwa a lokuta daban daban.

Hari mafi tsanani cikin wadannan kwanaki shi ne wanda 'yan bindigar suka kaddamar da sanyin safiyar ranar Lahadi 29 ga wata, a wata kwalejin koyar da ayyukan noma dake jihar Yobe. An ce, maharan sun bude wuta kan dalibai wadanda ke dakunan kwanansu a lokacin, wanda hakan ya haddasa rasuwar kimanin yara matasa 47, da mafiya yawansu shekarunsu ba su wuce 18 zuwa 22.

Kwana guda kafin aukuwar wannan hari, wasu mutanen su 11 su ma sun rasa rayukansu, bayan da wasu maharan suka kai farmaki kauyen Zangang, dake jihar Kaduna, kauyen da mahukuntan kasar suka ce, a bana kawai, ya fuskanci makamantan wadannan hare-hare har sau 3.

Har ila yau tsakanin ranar Laraba da Alhamis, wasu 'yan bindigar sun hallaka mutane a kalla 27 a wasu kauyuka daban-daban dake jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriyar.

Wadannan hare-hare dai na dada tabbatar da barazanar da jagorancin kungiyar Boko Haram wato Sheik Abubakar Shekau ya yi, ta ci gaba da aiwatar da karin hare-hare har sai kungiyar ta cimma burinta na kafa tsarin Islama a kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China