Mahukuntan jihar Zamfara dake arewa maso yammacin tarayyar Najeriya sun ce, kimanin mutane 160 ne suka hallaka cikin watanni 3 da suka gabata, sakamakon farmakin da 'yan bindiga ke kaiwa wasu kauyukan dake sassan jihar.
Gwamnan jihar ta Zamfara Abdulazez Yari ne ya bayyana hakan ga 'yan majalissar dokokin jihar. Ya ce, rahotanni sun kuma tabbatar da sace wasu matan aure 10, ba ya ga shanu da sauran dabbobi da maharan kan yi awon gaba da su yayin da suka kai irin wadannan hare-hare.
GwamnaYari ya kara da cewa, hakan ya haifar da rashin jituwa tsakanin al'umman da lamarin ya shafa da kuma tsagin mahukunta. Don haka ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da karin jami'an tsaro a jihar, kasancewar gwamnatin jihar ita kadai, ba ta da cikakken ikon shawo kan lamarin.
Tun dai cikin shekarar 2009 ne yankin arewacin tarayyar Najeriya ke shan fama da hare-hare, da mafiya yawansu ake danganawa da ayyukan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram, wadda ke fafitikar kafa tsarin shari'ar musulunci, tare da yaki da ilimin Boko. (Saminu)