Wani mutum da yake ikirarin shi ne shugaban kungiyar ta'addancin nan a Najeriya Boko Haram, Abubakar Shekau a ranar Laraban nan ya yi alkawarin cewa, kungiyarsa za ta kai karin hare-hare a arewacin kasar, har sai an komar bisa dokoki na musulunci a duk fadin kasar.
Shekau wanda a da aka yi shelar cewa, jami'an tsaro na soji sun kashe shi, ya aika wannan bayanin ne a cikin wani sakon bidiyo da aka fitar a Maiduguri, yana mai cewar, zai dakatar da mulkin demokradiya a kasar da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afrika baki daya.
Mutumin da aka nuno magoya bayansa na zagaye da shi rike da bindigogi ya kuma karyata bayanan da ke cewar, an harbe shi kuma magoya bayansa sun tsere da shi ta jirgin ruwa don nema masa magani.
Ya yi ikirarin cewar, kungiyarsa ke da alhakin harin da aka kai a garin Benisheik mai tazaran kilomita 50 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno, yana mai shelar cewa, kungiyar ta yi nasarar kai hari a unguwar Monguna, inda akwai barikin sojoji a wajen da kuma Benisheik da sauran garuruwa a zagayen Maidugurin. (Fatimah)