Rundunar soji a tarayyar Najeriya ta ce, ta hallaka wasu dakarun kungiyar nan ta Jama'atu Ahlussunnah Lidda'awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram su 10, sakamakon wani hari da ta kaddamar ta sama, kan maboyar 'yan kungiyar dake garin Mada, a karamar hukumar Konduga, da kuma Damboa, duka a yankin birnin Maiduguri dake jihar Borno.
Da yake karin haske ga kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua, don gane da aukuwar wannan lamari, kakakin rundunar sojin kasar dake jihar ta Borno Laftana Kanal Sagir Musa, ya ce, farmakin da suka kaddamar ya ba su damar kwace wasu makamai da suka hada da manyan bindigogi kirar AK47, da kuma harsasai. Har ila yau rundunar ta kone wasu baburan hawa da sauran kayayyaki da ake zargin 'yan kungiyar na amfani da su wajen kaddamar da hare-hare.
A makon da ya gabata ma dai sai da dakarun rundunar sojin ta Najeriya ta bayyana cewa, ta samu nasarar farma 'yan kungiyar ta Boko Haram, a wani hari da ya sabbaba rasuwar 'ya'yan kungiyar su 50. Sai dai kawo yanzu rahotanni na nuna cewa, hare-haren 'yayan kungiyar na dada karuwa a yankunan dake kan iyakokin jihar ta Borno, wadda ke arewa maso gabashin kasar ta Najeriya. (Saminu)