Jami'in da ke kula da Bataliyan da ke gudanar da ayyuka na musamman a Najeriya, Laftana kanar Beyidi Martins, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ranar Lahadi cewa, jami'an tsaro na sojoji sun kama wasu mutane 11 a jihar Adamawa da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne a wani samame da suka kaiwa 'yan kungiyar.
Laftana kanar Beyidi Martins ya ce, an kama wadanda ake zargin ne a garin Machika ranar Asabar, inda aka garzaya da 6 daga cikin wadanda ake zargin zuwa wani gari da ke kusa da Maiduiguri, biyar daga cikinsu kuma aka kaisu garin Mubi.
Jami'in ya ce, biyu daga cikin 'yan kungiyar ta Boko Haram, sun mutu ranar Lahadi sakamakon raunukan da suka samu, kana daya daga cikinsu yana raye inda ake masa tambayoyi, yayin da guda 3 suka ji rauni sakamakon turjiyar da suka nuna wa sojojin. (Ibrahim)