in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana zaman taron kasa da kasa a N'Djamena kan tsaro a yankin Sahel
2013-09-11 10:25:35 cri

Shugabannin hukumomin leken asiri na kasashen yankin Sahel na wani zaman taron tun ranar Talata a birnin N'Djamena na kasar Chadi domin tattauna batun matsalar tsaro dake adabar wannan shiyya, da kuma karfafa karfin aiki a fannin leken asiri da samar da bayyanai da kuma tabbatar da tsaro a wadannan kasashe. 'Matsalar Boko Haram dake kamari da makarrabanta dake kan iyakoki, yawaitar wasu sabbin kalubalolin tsaro dake nasaba da manyan laifuffuka, tsatsauren ra'ayin kishin islama da kuma garkuwa da mutane sun kasance muhimman matsaloli dake kawo babbar barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Sahel.' in ji sakataren kasar Chadi a ofishin ministan cikin gida da tsaro, Mahamat Adji a cikin jawabinsa na bude taron.

A cewarsa, wannan haduwa ta N'Djamena wata babbar dama ce domin yin shawarwari masu fa'ida kan matsalar tsaro da kuma daukar matakan da suka wajaba domin fuskantar wadannan kalubaloli.

A nasa banagre, kwamishinan tsaro da zaman lafiya na kungiyar AU, Ramdane Lamamra ya nuna cewa, barazanar da zaman lafiya da kwanciyar hankali suke fuskanta matsala ce ta kasa da kasa ke nan, ya kamata a tanadi duk wasu hanyoyin dakile wannan matsala tare. Zaben kasar Chadi da birnin N'Djamena domin karbar wannan taro ya shaida wani yabon kasa da kasa kan kasar Chadi bisa kokarin da ta bayar wajen kwato arewacin kasar Mali daga hannun kungiyoyin kishin islama da kungiyoyi masu rike da makamai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China