in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana za ta shirya taruka biyu na kasa da kasa gabannin babban taro kan sadarwa ta duniya
2013-09-27 09:53:11 cri

Gwamnatin kasar Ghana ta sanar a ranar Alhamis din nan 26 ga wata cewa, za ta shirya manyan taruka biyu na kasa da kasa kafin babban taro na kungiyar cigaban sadarwa ta duniya da za'a yi a shekara mai zuwa.

Taron ciyar da yankin na Afrika, za'a yi shi ne a ranar 1 ga watan gobe na Oktoba, sannan na biyun kuma na shirye-shiryen Afrika game da babban taron, za a yi shi a ranar 2 zuwa 4 ga watan na oktoba, za a gudanar da dukkansu a cibiyar taro ta kasa da kasa dake Accra, babban birnin kasar.

Wadannan taruka biyu za su share fagen ga shirye-shiryen da wakilai daga nahiyar Afrikan wajen tsai da matsaya daya, su tsai da shawara a kan jadawalin babban taron na kasa da kasa karo na shida da za'a yi daga ranar 31 ga watan Maris zuwa 11 ga watan Afrilu na shekara ta 2014, kamar yadda madam Victoria Hamah, karamar ministan sadarwa ta kasar ta sanar.

Ta yi bayanin cewa, wannan taro na yankunan da za'a yi, kungiyar sadarwar ta duniya ce ta dauki nauyinsa domin a cimma nasarar ba da tsari mai kyau ga yankuna, a kuma samar da lokacin da jami'ai za su hadu da juna wajen tattauna abin da za su gabatar lokacin babban taro na kasa da kasa.

Madam Victoria ta yi bayanin cewar, kasancewar Ghana a cikin wannan kungiyar sadarwar duniya ya ba ta wani matsayi na zama, inda ya fi cancanta a yi irin taron a nahiyar Afrika baki daya domin tattauna bukatun da sauran kasashe ke da su da za su gabatar lokacin taron. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China