An yi kira ga magoya bayan babbar jam'iyyar adawa ta NPP a Ghana, da su kwantar da hankulansu, su kuma kauracewa daukar duk wani mataki da ya sabawa doka, sakamakon watsi da karar jam'iyyar da babbar kotun kasar ta yi a ranar Alhamis.
Da yake gabatar da wannan kira ga dinbin magoya bayansa, jagoran 'yan adawa, kuma 'dan takarar jam'iyyar ta NPP a babban zaben kasar da ya gabata a bara, Nana Akufo-Addo, wanda tun da farko, shi ne ya shigar da karar dake kalubalantar sahihancin zaben da ya baiwa shugaba John Dramani Mahama nasarar ci gaba da juya akalar kasar ta Ghana, ya ce, bai amince da sakamakon shari'ar ba, sai dai ba shi da niyyar daukaka kara.
Akufo-Addo, ya yi fatan cewa, nan gaba kasar ta Ghana za ta samu kyakkyawan sauyi ta fuskar yadda zabuka ke gudanarwa. Ya ce, sun riga sun kafa wani sahihin ginshiki da 'yan baya za su dora a kansa. Don haka ya yi kira ga jam'iyyun kasar da su kau da bambance-bambance dake tsakaninsu.
Dan takarar jam'iyyar ta NPP ya kuma yiwa shugaba Mahama fatan alheri, tare da kira da a dauki dukkanin matakan da suka dace domin daukaka matsayin kasar.
Shugaba Mahama wanda ya hau kan kujerar jagorancin kasar ta Ghana bara, biyowa bayan rasuwar shugaba John Atta Mills, a yanzu haka zai shafe shekaru 4 yana jagorancin kasar, kamar dai yadda kundin mulkin kasar ya tanada. (Saminu)