A cikin jawabin da Ban ki-moon ya yi, yayin da ya halarci taron, ya ce, bayan da aka tsara shirin MDGs, an samu goyon baya daga kasashen duniya, kuma sun yi alkawuran da ba a taba ganin irinsu ba, wadanda suka taimaka ga samun babban ci gaba, amma duk da haka, yanzu, akwai bambanci da ke tsakanin kasashe da yankuna daban daban na duniya wajen cimma buri 8 da ke kunshe cikin shirin na MDGs, kana akwai mutane sama da biliyan 1 da ke rayuwa cikin kangin talauci, kuma sauran shekaru 2 da rabi cikin wa'adin da aka tsara na cimma wannan burin.
Ban ki-moon ya ce, akwai kalubale sosai don cimma burin, amma mun yi imani cewa, za a kammala wadannan ayyuka cikin wannan lokaci da aka tsaida. Haka kuma, gwamnatocin kasashen duniya, da bankin duniya da hukumomi masu zaman kansu da sauran hukumomi sun dauki sabon alkawari, wato suna fata za su kara saka jarin da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 2.5 don cimma burin. Dole ne kasashen duniya su cimma burin MDGS, don kawo wani harsashi mai kyau wajen tsara shirin samun dauwamammen ci gaba bayan shekarar 2015.
Shugabanni da kusoshin gwamnatoci da wakilan kasashen duniya sun cimma matsaya guda tsakaninsu a yayin taron, inda suka jaddada kokarin cimma burin na MDGs, tare da dora muhimmanci sosai game da matsalar bambanci da rashin daidaito wajen samun ci gaba da ke kasancewa a yanzu. Haka kuma, mahalartar taron sun amince da kiran taron koli a watan Satumba na shekarar 2015, don tsara shirin samun ci gaba bayan shekarar 2015.(Bako)